Isa ga babban shafi
Turkiya-Jamus-Armenia

Turkiya ta janye Jekadanta daga Jamus kan kisan Armeniyawa

Kasar Turkiya ta janye jekadanta daga Jamus bayan majalisar kasar dokokin kasar ta kada kuri’ar dake nuna cewa Turkiya ta yiwa Armeniyawa kisan kiyashi a karkashin daular Othman.

Mutane da dama da suka mamaye harabar majalisar Jamus sun yi farin ciki da amincewa da matakin
Mutane da dama da suka mamaye harabar majalisar Jamus sun yi farin ciki da amincewa da matakin REUTERS/Stringer
Talla

Kudirin dai ya samu gagarumin rinjaye a majalisar Jamus yayin da dan majalisa guda ne kawai ya kada kuri'ar kin amincewa da kisan kiyashin da aka yi wa Armenia da wasu kiristoci tsiraru a wajajen 1915 zuwa 1916 a zamanin daular othman.

Mutane da dama da suka mamaye harabar majalisar sun yi farin ciki da amincewa da matakin.

Haka ma gwamnatin Armenia ta yi jinjina ga Jamus musamman na jagorantar yin allawadai da kisan kiyashi a kan Armeniyawa.

Sai dai Turkiya ta la’anci matakin, wanda ta kira haramtacce, kamar yadda kakakin gwamnatin kasar kuma mataimakin Firaminista Numan Kurtulmus ya sanar a shafin Twitter.

Amincewa da kuridin dai zai dada dagula dangantaka tsakanin Turkiya da Jamus, inda yanzu haka gwamnatin Ankara ta janye jekadanta daga Berlin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.