Isa ga babban shafi
Duniya

Mutane miliyan 45 na rayuwar aikin bauta a duniya

Wani bincike ya nuna cewar akalla mutane miliyan 45 ke zama cikin aikin bauta a sassan duniya, kuma akasarin su na zama ne a Yankin Asia.

Cibiyar Walk Free Foundation ce ta gudanar da binciken tare da yin kira ga hukumomi su dauki mataki.
Cibiyar Walk Free Foundation ce ta gudanar da binciken tare da yin kira ga hukumomi su dauki mataki.
Talla

Rahotan kungiyar da ke yaki da bauta na shekarar 2016 ya gudanar da bincike a kasashe 167, inda ya tattauna da mutane 42,000 a harsuna 53, kuma binciken ya nuna cewar akwai bayi sama da kashi 28 sabanin adadin baya.

Kasashen da matsalar ta fi kamari sun hada da India da China da ke da sama da miliyan 3, Pakistan sama da miliyan 2, Bangladesh sama da miliyan daya da rabi, sai kuma Uzbekistan mai sama da miliyan guda.

Aikin bautar zamani ya hada da aje mutane suna aikin da basa so saboda bashi, ko yaudarar su ko kuma tilastasu saboda wata barazana ga rayuwar su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.