Kungiyar Lafiya Ta Duniya Ba Za Ta Kwace Gasan Olympics Daga Brazil Ba
Kungiyar Lafiya ta Duniya , WHO a takaice ta kawar da dukkan wani shakku cewa za'a zakuda da gasan wasannin Olympics daga birnin Rio De Janairo na kasar Brazil zuwa wani wajen saboda cutar nan dake sauya halittan jira-jirai da ake kira Zika.
Wallafawa ranar:
Wasu masana 150, da suka kunshi manyan likitoci da masu bincike da wasu kwararru ta fannin kiwon lafiya, ranar Juma'a data gabata, suka rubutawa kungiyar Lafiya ta Duniya, wata wasika dake bukatar a zakuda da gasan, ko kuma a jinkirta saboda annobar cutar Zika.
Suna masu cewa gudanar da gasan a birnin Rio De Janairo, gari na biyu da cutar ta yiwa illa, ganganci ne sosai.
Amma kuma Kungiyar Lafiya ta duniya tace zakudawa da gasan babu wani alfanu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu