Isa ga babban shafi
G7 a Japan, Duniya

Taron G7 a Japan

An fara taro na kwanaki biyu na Shugabannin manyan kasashen duniya 7 masu karfin tattalin arziki, a Japan.Mahalarta taron zasu tattauna batutuwan da suka shafi tattalin arziki, ta’adanci da al’amarin ‘yan gudun hijira da ake fama dasu, dama batun janyewar Britania daga cikin kungiyar kasashen Turai. 

Shugabanin kasashe masu karfin tattalin arziki a Duniya a taron Ise Shima na Japan
Shugabanin kasashe masu karfin tattalin arziki a Duniya a taron Ise Shima na Japan REUTERS/Jim Watson/Pool
Talla

Shugabannin kasashen Amurka, Britania, Faransa, Jamus , Italia, Canada da mai masaukin baki Japan ke halartan tattaunawan a yankin tsaunukan Ise Shima mai nisan kilomita 300 kudu maso yammacin birnin Tokyo.
An dauki tsauraran matakan tsaro a fadin kasar ta Japan, inda aka girka ‘yan sanda na musamman a tashoshin jiragen kasa da wurare masu muhimmanci gudun kada a fuskanci wata matsala.
Hukumomin kasar sun bayyana cewa ba zasu yi sake ba ganin irin barnan da ‘yan taadda sukayi a Paris da Brussels cikin shekarar data gabata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.