Isa ga babban shafi
Faransa

Manuel Valls na Faransa na ziyara a Isra'ila

A jiya lahadi ne Firaministan Fransa Manuel Valls ya rubanya kalaman nuna abota ga kasar Isra'ila tare da bayyana kiran taron zaman lafiya na birnin Paris tsakanin Yahudawa da Falasdinawa da cewa, amfanin kasar ta Isra'ila ne, kafin ya nanata bukatar son kawo karshen mulkin mallakar da Isra'ila ke yi wa Falasdinawan.

Firaministan Faransa Manuel Valls da takwarana na Isra'ila  Benjamin Netanyahu
Firaministan Faransa Manuel Valls da takwarana na Isra'ila Benjamin Netanyahu
Talla

Mr. Valls ya fara rikitacciyar ziyarar ta kwanaki uku ne a kasar Isra'ila da kuma a yankunan Falasdinawa, inda zai ziyarci bude tashar samar da wutar lantarki ta hasken rana da kamfanin EDF Energies na kasar Fransa ya gina, kafin ya gana da Faransawa da ke birnin Tel-Aviv, inda zai yi jawabi a gaban dalibai Faransawa da Yahudawan kasashe renon Faransa.

Mr. Valls dai ya bayanna cewa, dukkanin bangarorin ziyarar tasa su nada matukar muhimmanci.

Sai dai kuma maganar kokarin shirya zaman taron zaman lafiyar a birnin Paris shi ne abinda ya tsayawa Faransa a rai tun bayan cimma rashin nasarar da aka yi a yinkurin baya bayan nan da Amurka ta jagoranta a 2014.

Mr. Valls dai zai fuskanci gagarumar adawa ga manufar kasarsa akan Falasdinawa, wanda a kowanne lokaci Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ke zargi da daukar bangaranci.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.