MDD ta damu da halin da Burundi ke ciki
Majalisar dinkin duniya ta nuna matukar damuwa game da halin da kasar Burundi ke ciki da yadda ake kama mutane ana tsare su, da kuma yadda kasar Uganda da ke makwabtaka da ita ke koran ‘yan gudun hijira daga Burundi.
Wallafawa ranar:
Farhan Haq mai magana da yawun Majalisar dinkin duniya ya fadi cewa, hauhawan tarzoma da yadda ake tsare mutane ba kan gado na matukar bukatar sa ido sosai, kuma yanzu haka jamiai na sa ido sosai game da irin wainar da ake toyawa a kasar.
Hauhawan tarzomar da kama mutane ana tsarewa na zuwa ne a daidai wani lokaci da ake cika shekara guda da yunkurin da wasu sojoji suka yi na kifar da gwamnatin Pierre Nkurunziza.
Majalisar dinkin duniya na cewa, abin bukata shi ne, zama ayi sulhu a maimakon yadda ake yi tun bayan da shugaban kasar ya ayyana zarcewa da mulki da karfin tsiya.
A ranar juma'ar da ta gabata, mutane akalla 100 aka kama aka tsare su a birnin Bujumbura, a wani yunkuri na hana ‘yan adawa sakat a fadin kasar.
Ya zuwa yanzu mutane akalla 500 aka kashe yayin da wasu dubu 250 suka kaurace wa kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu