Isa ga babban shafi
Syria

Kasashen duniya na tattaunawa kan Syria

Manyan jakadun kasashen duniya na gudanar da taro a wannan Talata a birnin Vienna na kasar Austria domin tattaunawa kan yadda za a farfado da yunkurin samar da zaman lafiya a Syria. 

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry da takwaransa na Rasha Serguei Lavrov
Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry da takwaransa na Rasha Serguei Lavrov REUTERS/Leonhard Foeger
Talla

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da takwaransa na Rasha, Sergei Lavrov ke jagorantar zaman na yau.

Taron dai zai jaddada bukatar tsagaita musayar wuta a dukkanin fadin kasar ta Syria da kuma bai wa kungiyoyin agaji damar isar da kayayyakin jin kai ga yankunan da aka yi wa kawanya.

Kasar Amurka dai ta jaddada bukatarta ta ganin shugaba Bashar al Assad ya sauka daga mukaminsa, sai dai shugaban na Syria wanda ke samun goyon bayan Rasha da Iran, bai nuna wata alamar sauka daga kujerarsa ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.