Isa ga babban shafi
MSF-MDD

MSF zata kauracewa taron Jinkai na MDD

Kungiyar Likitoci ta MSF ta sanar da matsayinta na kauracewa taron Jinkai na Majalisar dinkin duniya, inda ta ce taron zai gaza wajen Matsin lamba ga Gwamnatoci dake kin taimakawa Mutanen da cuttuka ko yaki ke ritsawa da su.

Shugabar MSF Joanne Liun
Shugabar MSF Joanne Liun REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Kungiyar MSF ta ce ta cire rai kan taron, da ba zai shawo kan matsalolin da ake dashi a fanin jinkai da taimakon gaggawa ba, musamman a yankunan da ake fama da yake-yake ko anoba.

A sanarwa da ta fitar, MSF ta ce taron da za’ayi a isatanbul tsakanin ranakun 23 zuwa 24 ga watan mayu, ba zai cike gibin dake akwai kan barazanar anobar Ebola ba, da yankunan da yaki ya hana a shigar da kayan jinkai, da barazanar da jami’an kiwon lafiya ke fuskanta a yankuna da ake tafka rikici, da suka hada da Syria da Yemen da Sudan ta kudu.

MSF ta kuma bada Misalin fararren hula da ke neman tserewa amma aka datse su a iyakar Jordan, Turkiyya da Mecedonia a matsayin rashin imani ga ‘yan gudun hijira da bakin haure dake neman mafaka a Girka da Australia saboda tsaro.

Don haka tana furgaban cewa Taron zai gaza wajen tilastawa gwamnatocin kasashe, mutatan hakin daya rataya a wuyansu na jinkai, da batun sanya hannu kan dokar ‘yan gudun hijira da aka gagara sa hannu.

Taron irinsa na farko, ana saran halartar shugabanni kasashen duniya 45, da jami’an hukumomin MDD da kungiyoyin masu zaman kansu, inda zaa wasa kwakwalwa kan matakan daya dace a daukan kan taimakon jin kai a duniya.

MDD dai ta nuna rashin jindadinta da matakin MSF na bijirewa Taron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.