Isa ga babban shafi
Amurka

Kuskuren Likita shine abu na 3 dake haifar da mutuwa a Amurka

Wani Bincike a kasar Amurka ya ce kuskuren Likita ne abu na uku wajen haifar da mutuewar al’ummar kasar.

CC/Wikimedia Commons
Talla

Mujallar binciken kiwon lafiya ta ruwaito cewar a shekarar 2013 akalla mutane 250,000 suka mutu sakamakon rashin lafiya ko kuma raunin da suka samu amma basu samu kulawar da ta dace ba ko kuma ba’a basu maganin da ya dace da rashin lafiyar.

Rahotan ya ce adadin ya zarce wadanda suke mutuwa sakamakon cutar shanyewar jiki da kuma wadda ke da nasaba da cutar kwakwalwa.

Rahotan ya ce masu mutuwa sakamakon cutar bugun zuciya da sankara ce kawai suka zarce wadannan, wanda kowanne daga cikin su ke hallaka mutane 600,000 kowacce shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.