Isa ga babban shafi
Syria

Amurka da Rasha Sun Cimma Matsaya Game da Tsagaita Wuta a Aleppo na Syria

An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin da ake fafatawa mafi muni a yankin Aleppo na kasar Syria bayan an dauki lokaci ana ta jan kafa, yayin da rayukan bayin Allah ke ta salwanta.Yanzu haka Gwamnatin Shugaban Syria ta amince da a tsagaita wuta na tsawon sao'i  48 daga Alhamis.  

Jakadan MDD a sasanta rikicin Syria Staffan de Mistura
Jakadan MDD a sasanta rikicin Syria Staffan de Mistura REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Wata sanarwa daga ma'aikatar tsaron Amurka ta fitar tu da fari,  da sa hannun kakakin ma'aikatar Mark Toner, na gaskata cewa har an ga alamun tsagaita wuta zai fara aiki.

Sanarwan na cewa domin ganin dorewar yarjejeniyar Amurka da Russia na wani tsarin sa idanu sosai.

A makon jiya Amurka da Rasha sun amince su sa idanu sosai tsakanin yarjejeniyar da aka kulla da Dakarun Shugaba Bashar Assad da kuma ‘yan tawaye a yankin Latakia da Gabashin Ghouta amma kuma yankin Aleppo, babbar cibiyar kasuwanci, ba'ayi batun sa ba duk da cewa ana ta rasa rayukan jama'a.

Jami'an Rasha sun bayyana cewa ba zasu farma Dakarun Assad ba domin suna kokarin yakar ‘yan tawaye ne, amma kuma sakataren waje na Amurka John Kerry da kuma jakadan MDD a kasar Syria Staffan De Mistura sun hakikance cewa dole Rasha ta shiga batun tsagaita wuta a dukkan fadin kasar Syria, wanda aka amince tun watan biyu na wannan shekara.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.