Isa ga babban shafi
Syria

Rasha da Amurka na tattaunawa kan Syria

Kasashen Rasha da Amurka sun ce, suna tattaunawa don ganin an kawo karshen kazamin tashin hankalin da ake samu a garin Aleppo na kasar Syria. 

Shugaban Rasha, Vladmir Putin da Barack Obama na Amurka
Shugaban Rasha, Vladmir Putin da Barack Obama na Amurka REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Fadan da aka kwashe sama da mako guda ana yi a Aleppo ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 250, abinda ya jefa shirin tsagaita wutar majalisar dinkin duniya cikin mawuyacin hali.

Ranar Asabar Rasha ta ce, ba za ta hana sojojin Syria kai hari kan 'yan tawayen da ba sa cikin yarjejeniyar tsagaita wutar ba, amma bayan tattaunawa da jami’an Amurka, hafsan sojin kasar Janar Sergei Kuralenko ya ce, ana tuntubar masu hannu a rikicin don ganin an kawo karshen fadan.

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry ya isa Geneva inda ake saran zai tattauna da Jakadan majalisar dinkin duniya, Stefan de Mistura da Jakadun kasashen Saudi Arabia da Jordan don kawo karshen fadan.

Mutane 253 aka kashe a fadan da ya barke tun ranar 22 ga watan jiya, cikin su har da kananan yara 49 sakamakon harba makaman roka da harin sama.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.