Isa ga babban shafi
Australia

Jam'iyyar Freedom ta lashe zaben Australia

Dan takarar jam’iyyar Freedom Party mai adawa da shigar baki a Australia ya lashe zagayen farko na zaben shugabancin kasar da aka gudanar a yau Lahadi.

Norbert Hofer na jam'iyyar Freedom Party mai ra'ayin rikau
Norbert Hofer na jam'iyyar Freedom Party mai ra'ayin rikau REUTERS/Heinz-Peter Bader
Talla

Norbert Hofer ya samu kashi 36 cikin 100 na kuri’un da aka kada, inda abokan hamayyarsa daga jam’iyyun kawance biyu da ke mulkin kasar suka gaza samun wani kaso da zai basu damar shiga zagaye na biyu na zaben wanda za a yi a ranar 22 ga watan Mayu mai zuwa.

Ana dai kallon wannan nasara ta Hofer a matsayin wani abu mai cike da tarihi a jam’iyyar Freedom Party mai ra’ayin rikau, lura da cewa ba ta tana samun yawan kuri’u kamar a wannan karan ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.