Isa ga babban shafi
Belgium

Maharan Brussels da Paris sun yi tanadi- ISIS

Kungiyar ISIS ta bayyana cewa, Khalid da Ibrahim El Bakraoui da suka kai harin Belgium, sun tanadi makamai da kansu da suka hada da bama-bamai musamman don kaddamar da hare haren Brussels da Paris.

Hoton mutanen da suka kai harin Brussels na Belgium
Hoton mutanen da suka kai harin Brussels na Belgium AFP PHOTO / BELGIAN FEDERAL POLICE
Talla

A sanawar da ta fitar a wannan Laraba a jaridarta mai suna Dabiq, kungiyar ISIS mai da’awar jihadi ta tabbatar cewa, kahlid da dan uwansa Ibrahim El Bakraoui, da su aka yi dukkanin shirye shiryen kaddamar da wadannan haren haren na biranen Bruseesls da Paris.

Wadannan 'yan uwan junan, sun tanadi makamai da suka hada da bama-bamai domin hare haren da suka yi sanadin mutauwar jama’a da dama kamar yadda ISIS ta ce.

Matukar dai aka tababtar da ikirarin kungiyar, to hakan na nufin cewa, Khalid da Ibrahim sun taka rawa fiye da kowa a harin Paris, sabanin yadda aka zaci a farko.

Jaridar ta ISIS, ta kara da cewa Najim Laachraoui wanda ya tarwatsa kan sa tare da Ibrahim Bakraoui a harin kunar bakin wake a filin jirgin saman Zaventem na Brussels, shi ma ya tanadi bamai bamai da kansa saboda wannan harin kuma da shi aka kai harin Paris.

Khalid El Bakraoui kuwa, shi ne wanda ya tayar da bama –bamai da ke kunshe a rigarsa, inda ya kashe mutane 32 a tashar jirgin kasan Brussels.

Harin Paris dai da wadannan mutane suka kai a watan Nuwamban bara a Paris, ya hallaka mutane 130.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.