Isa ga babban shafi
peru

Fujimori na kan gaba a zaben Peru

‘Yar tsohon shuggaban Peru Alberto Fujimori wanda ke tsare a gidan yari saboda kisan al’ummar kasar, Keiko Fujimori, ita ce ke sahun gaba a zaben shugabancin kasar da aka gudanar a jiya Lahadi.

Keiko Fujimori na murnar samun nasara a zaben shugaban kasar Peru
Keiko Fujimori na murnar samun nasara a zaben shugaban kasar Peru REUTERS/Mariana Bazo
Talla

Fujimori dai mai shekaru 40 a duniya, na  gaban abokin hamayyarta Pedro Pablo Kuczynski mai shekau 77 a duniya.

Fujimori ta samu kashi 39.18 cikin 100 na kuri’un da aka kada yayin da Kuczynski  ya samu kashi 24.25 cikin 100 kamar yadda hukumar zaben kasar ta bayyana.

To sai dai za a je zagaye na biyu a zaben lura da cewa Fujimori wadda ta yi karatu a Amurka ta gaza samun kashi 50 cikin 100 na kuri’un abinda zai ba ta damar lashe zaben kai tsaye.

A ranar 5 ga watan Yuni mai zuwa ne za a gudanar da zagaye na biyu na zaben, yayin da al’ummar kasar ke bukatar canji.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.