Isa ga babban shafi
Madagascar

Fira Ministan Madagascar Ya Karyata Yayi Murabus

Shugaban kasar Madagascar Hery Rajaonarimampianina jiya Juma'a ya sanar da murabus din Fira Minista kasar Jean Ravelonarrivo, bayan sun kwashe makonni ana zaman doya da manja.

Fira Ministan Madagascar Jean Ravelonarivo
Fira Ministan Madagascar Jean Ravelonarivo AFP PHOTO / RIJASOLO
Talla

Sai dai kuma tun ba’a kai koina ba  Fira Ministan ya karyata cewa yayi murabus.

Dangantaka tsakanin Shugaban kasar da Fira Minista Jean Ravelonarrivo babu dadi, saboda takardama gameda matsalolin da jamaa ke fama da rashin hanyoyi masu kyau da yawaitan laifuka a kasar.

Ofishin Shugaban kasar sun bayyana cewa sun karbi takadan murabus din Fira Minista,  amma kuma nan da nan Ofishin  Fira Ministan  suka ce karya ne.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.