Isa ga babban shafi
US-CUBA

Obama ya sauka a Havana

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya isa kasar Cuba a wata ziyara tarihi, wanda ke jaddada kawo karshen zaman doya da manja tsakanin kasashen biyu na tsawon shekaru 50.

Shugaban kasar Amurka Barack Obama a fillin jirgin saman Havana
Shugaban kasar Amurka Barack Obama a fillin jirgin saman Havana REUTERS/Enrique De La Osa
Talla

Shugaba Barack Obama da matarsa da ‘ya’yansu biyu ne suka isa birnin Havana na Cuba a wannan ziyara da za ta dauke su kwanaki uku

Ziyarar dai ta kasance karo na farko da shugaban kasar Amurka mai ci ke kaiwa Cuba tun bayan da mayakan tsohon shugaba Fiedel Castro suka kwace mulki daga hannun Fulgencio Batista a shekarar 1959

Kuma Wannan ziyara itace karo na farko tun ziyarar Shugaba Calvin Coolidge shekaru 88 da suka gabata

A yau litinni ake saran Mista Obama da ke wa’adinsa na karshe a Mulki Amurka, ya gana da takwaransa Raul Castro na Cuba, kana zai hallarci wasan Baseball kafin ya bar kasar a gobe talata.

A na saran wannan ziyara ta kawo karshen zaman doya da manja dake kawai tsakanin kasashen tsawon shekaru 50 yanzu

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.