Isa ga babban shafi
Malaysia

Za a yi bincike kan buraguzan jirgin Malaysia

Hukumomin Malaysia sun bayyana cewa, a yau Alhamis za a aika karikitan jirgin saman da aka gano a gabar ruwan kasar Mozambique zuwa Australia domin gudanar da bincike da nufin gano alakarsu da jirgin Malaysia samfurin Boeing 777 da yi batan dabo shekaru biyu da suka gabata.

Kwararru za su yi bincike don gano musabbabin hadarin jirgin Malaysia dauke da fasinjoji 239 shekaru biyu da suka gabata.
Kwararru za su yi bincike don gano musabbabin hadarin jirgin Malaysia dauke da fasinjoji 239 shekaru biyu da suka gabata. 法新社
Talla

Ana kyautata zaton buraguzan jirgin za su taimaka wajan gano musabbabin hadarin jrigin na Malaysia dauke da mutane 239.

Ministan sufurin Malaysia, Liow Tiong Lai ya ce, binciken farko ya nuna cewa, akwai yiwuwar karikitan na jirgin ne mai lamba MH370 wanda ya bata a ranar 8 ga watan Maris na shekara ta 2014 bayan ya taso daga birnin Kuala Lampur, inda ya nufi hanyar Beijing na kasar China.

Kwararru daga kasashen Australia da Malaysia da wasu kasashen duniya ne za su gudanar da bincike akan buraguzan .

Shekaru 2 da faruwar wannan hatsari amma har yanzu batan jirgin na ci gaba da zama wani abin al’ajabi a tarihin hadarin jiragen fasinja a duniya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.