Isa ga babban shafi
FIFA

FIFA ta dakatar da Valcke na tsawon shekaru 12

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta dakatar da tsohon sakatare Janar dinta Jarome Valcke na tsawon shekaru 12 kan badakalar sayar da tikicin shiga kallon wasannin gasar cin kofin duniya.

Tsohon Sakatare Janar na Jerome Valcke
Tsohon Sakatare Janar na Jerome Valcke AFP/AFP/
Talla

Kwamitin da’a na hukumar ya fadi a cikin wata sanarwa cewa Valcke wanda aka tube daga mukaminsa a watan jiya an kuma dakatar da shi shiga sha’anin kwallon kafa na tsawon shekaru 12.

Tun tuni ne Bafaranshen mai shekaru 54 ke musanta laifinnsa na sayar da tikicin shiga kallon wasannin gasar cin kofin duduniya da aka gudanar a Brazil a 2014 ta bayan fage.

Hukumar FIFA kuma ta ci shi tarar kudi Fam dubu Saba’in da dari takwas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.