Isa ga babban shafi
Rasha

Rasha ta tsara yadda za a tsagaita wuta a Syria

Kasar Rasha ta shata wani tsari na musamman kan cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta a rikicin Syria, wannan kuma na zuwa ne kafin soma tattauna yadda za a shawo kan rikicin kasar tsakanin ministocin harakokin waje 17 a birnin Munich na Jamus.

Sakataren harkokin wajen Rasha Serguei Lavrov
Sakataren harkokin wajen Rasha Serguei Lavrov REUTERS/Maxim Shemetov
Talla

Ministan harakokin wajen Rasha Sergei Lavrov yace sun gabatar da tsarin yadda za a cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta, kuma ministan ya fadi haka ne kafin soma tattaunawarsa da takarawansa na Amurka John Kerry a birnin Munich na Jamus.

Sai dai Rasha tace tana jiran ta ji ta bakin Amurka kan daftarin da ta tsara kafin ta gabatar da shi ga taron gungun kasashen da ke kiran kansu masu taimakawa Syria.

John Kerry da Sergie Lavrov dai na jagorantar taron ministocin harakokin wajen kasashe 17 ne a Munich domin samo zaren warware rikicin Syria.

Taron kuma na zuwa ne a yayin da Majalisar Dinkin Duniya tace mutane 51,000 sun fice yankin Aleppo saboda luguden wutar da dakarun gwamnatin Syria ke yi tare da taimakon hare haren sama na jiragen yakin Rasha da Iran.

Wannan ne kuma ya sa kasashen yammacin ke ganin dalilin kawo cikas ga tattaunawar da aka shirya a Geneva da kuma samun karin 'yan gudun hijirar da ke ficewa daga kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.