MDD-Faransa-Britaniya
An bukaci Rasha ta kawo karshan hare-haren ta a Aleppo
Kasashen Faransa da Birtaniya da kuma kawayen su da ke kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya sun bukaci Rasha ta kawo karshen hare haren da ta ke kaiwa Aleppo dan ganin an kaiwa mutanen Yankin kayan agaji.
Wallafawa ranar:
Talla
Jakadan Faransa a Majalisar Francois Delattre ya ce ba wani taimako suke neman daga wajen kasar ba sai dai kawai tuna mata hakkin dake kan ta.
Kasashen New Zealand da Spain suka bukaci gudanar da taron dan nazari kan halin da jama’ar Aleppo ke ciki dangane da hare haren da gwamnatin Syria da Russia ke kaiwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu