Isa ga babban shafi
MDD-Korea ta Arewa

Roka: Amurka da China za su mayar da martani ga Koriya ta arewa

Shugaban kasar Amurka Barack Obama da takwaransa na China Xi Jinping, sun amince su mayar da martani ga takalar da Koriya ta arewa ke yi dangane da shirinta na harba makamin Roka. 

Sugaban kasar Koriya ta arewa Kim Jong Un na shrin harba Roka a cikin wannan watan na Fabairu
Sugaban kasar Koriya ta arewa Kim Jong Un na shrin harba Roka a cikin wannan watan na Fabairu Reuters/路透社
Talla

Shugabannin biyu sun jaddada muhimmancin mayar da martani na kasa da kasa kan Koriya ta arewa wadda a yanzu haka ake zargin ta fara shirye shiryen harba Rokan.

A cikin wannan makon ne gwamnatin kasar ta sanar da wannan shriin, al-amarin da kasashen yamma suka kalla a matsayin yunkurin gwajin makami mai linzami a fakaice, abinda kuma ya saba wa dokokin kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya.

A ranar 6 ga watan Janairun wannan shekarar ne , Koriya ta arewa ta yi gwajin makamin Nukliya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.