Amurka
Amurka ta yaba da matakin Saudiya kan yaki da IS
Ma’aikatar tsaron Amurka ta yi marhaba da alwashin da Saudiya ta yi na yakar kungiyar IS ta kasa a Syria.
Wallafawa ranar:
Talla
Amurka ta dauki tsawon makwanni ta na kiran kawayanta daga kasashe 65 da ta ke jagoranta a yaki da IS a Syria da Iraqi, da su kara kaimi wajen bayar da gudun mawa, yayin da a cikin watan jiya sakataren tsaron Amurkan, Ashton Carter ya caccaki kasashen da ba su tabaka komai ba.
Mr Cater zai gana da hukumomin tsaron Saudiya a makon gobe a birnin Brussels na Belgium, inda ake sa ran tattaunawa kan tsare-tsaren kawar da kungiyar IS.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu