Isa ga babban shafi
Afghanistan

Messi na son haduwa da masoyin shi a Afghanistan

Gwarzon Dan wasan duniya Lionel Messi na Barcelona ya bayyana fatar haduwa da wani karamin yaro dan kasar Afghanistan wanda aka wallafa hoton shi a Intanet sanye da rigar leda da sunan dan wasan na Argentiina.

Dan shekaru 5 Murtaza Ahmadi sanye da rigar Leda da sunan Messi dan wasan Argentina
Dan shekaru 5 Murtaza Ahmadi sanye da rigar Leda da sunan Messi dan wasan Argentina lexpress.fr
Talla

Hoton Yaron mai suna Murtaza Ahmadi dan shekaru 5 a lardin Ghazni na Afghanistan ya ja hankalin mutane a Intanet.

Dan uwansa ne ya hada masa rigar leda mai kalar fari da bula wato Tutar Argentina tare da rubuta sunan Messi da lamba 10, sannan ya tura hoton a Facebook.

Duk da yaron da kwallon ragga ya ke kwallo amma ya nemi a saya ma shi rigar Messi amma mahaifin shi baya da hali.

Bayan yayan Murtaza ya saka hoton a facebook, nan take mutane suka fara yada hoton a shafukansu har zuwa twitter.

Yanzu haka kuma mahaifin Messi ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa cewa suna tattaunawa da hukumar kwallon Afghanistan kan hanyoyin da Dan wasan na duniya zai gana da yaron.

Sau biyar Messi na lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.