Isa ga babban shafi
Syria

'Yan adawar Syria za su halarci zaman sulhu a Geneva

‘Yan adawar Syria za su halarci zaman sasanta rikicin kasar da majalisar dinkin duniya ke jagoranta a birnin Geneva na kasar Switzerland, abinda ya kawo karshen barazanar da suka yi a farko na kin halartar zaman. 

Ana sa ran zaman sasanta rikicin ya kawo karshen yakin shekaru 5 a Syria.
Ana sa ran zaman sasanta rikicin ya kawo karshen yakin shekaru 5 a Syria. REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Sanarwa da kwamitin kolin sasanta rikicin Syria ya fitar, ta jaddada cewa ‘yan adawar za su aika wakilai 30 zuwa 35 birnin Geneva domin shiga tattaunawar amma ba da nufin cimma wata yarjejeniya ba.

Tuni dai kasashen Saudiya da Amurka suka yi marhaba da shawar da bangaren adawar ya yanke na shiga tattauawar kawo karshen yakin shekaru biyar a Syria.

A jiya jumma’a ne wakilan gwamnatin shugaba Bashar al Assad suka isa Geneva, inda suka yi ganawarsu ta farko da manzan musamman na majalisar dinkin duniya a Syria, Staffen de Mistura.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.