Isa ga babban shafi
Faransa

Lagarde za ta nemi wa’adi na biyu a IMF

Shugabar hukumar bada lamuni ta duniya IMF Christine Lagarde ta sanar da kudirin neman wa’adin shugabanci na biyu a yau Juma’a bayan samun goyon baya a kasashen Turai da China.

Christine Lagarde, Shugabar hukumar bada lamuni ta duniya IMF
Christine Lagarde, Shugabar hukumar bada lamuni ta duniya IMF Reuters
Talla

Lagarde ta sanar da matakin tsayawa takarar ne a wata tattaunawa ta musamman da ta yi da kafar Telebijin ta France 2.

Ta ce ta yanke shawarar tsayawa takara ne bayan samun goyon baya daga manyan kasashe da suka hada da Faransa da Birtaniya da Jamus da China.

A watan Yuli ne wa’adin shugabancinta zai kawo karshe, kuma yanzu hukumar IMF ta fara karbar ‘Yan takara da zasu jagorance ta nan da shekaru biyar.

Lagarde dai ta fuskanci kalubale na tabarbarewar tattalin arzikin Turai musamman rikicin bashin kasar Girka, kuma yanzu haka tana fuskantar bincike kan alakarta da attajirin Faransa Bernard Tapie, a lokacin da tana ministan kudi, zamanin mulkin Nicolas Sarkozy.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.