Isa ga babban shafi
Saudiya-Iran

Wasu Aminnan Saudiya sun katse hulda da Iran

Bayan Saudiya ta yanke huldar diflomasiya da kasuwanci da Iran kan kona ofishin jekadancinta a Tehran sakamakon kisan Malamin Shi’a da Saudiya ta yi, yanzu haka kuma kawayenta irinsu Bahrain da Sudan sun sanar da katse huldarsu da Iran.

Shugaban Sudan Omar Hassan al Bashir
Shugaban Sudan Omar Hassan al Bashir
Talla

Daular Larabawa ma ta sanar da sassauta dangantakar da ke tsakaninta da Iran.

Wannan ke tabbatar da takaddama tsakanin manyan kasashen biyu a gabas ta tsakiya  na dada fadada ganin yadda kasashen da ke goyan bayan Saudi ke ci gaba da katse hulda da Iran kan abin da suka danganta a matsayin katsalandan da kasar ke yi ga harakokin cikin gidan Saudiya.

Dukkanin aminnan Saudiya kasashen Sunni ne, wadanda suka dade suna samun sabani da muradun Iran da ke bin akidar Shi’a.

Tuni Saudiya ta ba jami’an Diflomasiyar Iran kwanaki biyu su fice daga kasarta.

Amurka da kasashen Turai sun bukaci bangarorin biyu su bi hanyoyi na lalama domin sasanta sabanin da ke tsakaninsu yayin da kasashen na yammaci ke fargaba ga kokarin da ake wajen samar da zaman lafiya a gabas ta tsakiya musamman kasashen Syria da Yemen.

Sannan rikici tsakanin Saudiya da Iran na iya haifar da barkewar rikici tsakanin ‘Yan Shi’a da Sunni a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.