Isa ga babban shafi
Duniya

Shugabannin duniya sun aike da sakonnin sabuwar shekara

Shugabannin kasashen duniya sun aike da sakonni daban–daban zuwa ga al’ummominsu dangane da shiga wannan shekara ta 2016.

Taron shugabannin duniya
Taron shugabannin duniya Reuters/路透社
Talla

Ta’addancin da kuma kawarar bakin haure, su ne muhimman batutuwan da shugabannin kasashen Turai suka fi mayar da hankali a jawaban nasu na bana.

Duk da barazanar kai harin ta’addanci da aka yi fargaba a birnin Munich lokacin bukukuwan sabuwar shekarar, Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta jaddada matsayinta na bai wa bakin haure damar shiga kasar a cikin wannan shekara.

Batun alakar da ke tsakanin Birtaniya da Kungiyar Turai, shi ne abinda ya fi jan hankali a jawabin firaminista David Cameron, yayin da shi kuma Francois Hollande na Faransa ke cewa shekara ta 2016 za ta kasance ta aiki wurjanjan domin yaki da ‘yan ta’adda a ciki da wajen kasar.

Su ma shugabannin Afirka sun aike da sakonni zuwa ga al’ummominsu, inda shugaban Chadi Idris Deby ya yi kira ga kasashen duniya da su taimaka a fadan da ake yi da Boko Haram, kamar dai yadda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kuduri aniyar yakar wannan kungiya da ta yi sanadiyyar daidaita mutane sama da milyan biyu a kasar.

A kasashen Nijar, Jamhuriyar Dimokurdiyar Congo, Gabon da Congo Brazzaville, batun zabubukan da ake shirin gudanarwa ne suka fi jan hankula a jawaban shugabannin kasashen, yayin da Shugaban Guinea Conakry Alpha Conde ya taya al’ummar kasar murnar kawar da cutar Ebola.

A Cote D’ivoire Kuwa Alassan Ouattara ne ya sanar da yin sassauci ga fursunoni dubu uku da 100 da aka yankewa hukunci saboda aikata laifufuka masu nasaba da rikicin zaben kasar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.