Isa ga babban shafi
ebola

An kawar da cutar Ebola a duniya- WHO

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce an yi nasarar kawar da Ebola a duniya bayan tabbatar da babu wani mai dauke da cutar a kasar Guinea wacce ta kasance kasa ta karshe cikin kasashen yammacin Afrika guda uku da cutar ta yi kamari a tsawon shekaru biyu.

AFP Photo/Dominique Faget
Talla

A ranar Talata ce hukumar lafiya ta duniya WHO ta sanar da kawo karsshen Ebola a kasar Guinea inda cutar ta fara bulla kafin ta bazu zuwa kasashen Liberia da Saliyo har zuwa Najeriya da Mali.

Hakan dai na nufin babu sauran cutar Ebola a duniya bayan kawar da cutar baki daya a kasashen Liberia da Saliyo da kuma Guinea a yanzu yayin da kasashen suka kasance ba shiga ba fita saboda Ebola.

Kimanin mutane 2,500 Ebola ta kashe a Guinea bayan ta bulla a 2013 kuma tun lokacin zuwa yanzu hukumar lafiya ta WHO ta ce, adadin mutane 11,300 suka mutu daga cikin 29,000 da suka kamu da cutar.

Ebola dai cuta ce mai yin kisa cikin hanzari, kuma wani jinjirin yaro ne mutum na karshe da aka tabbatar da warke warsa daga cutar Ebola a Guinea a ranar 16 ga watan Nuwamba.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.