Isa ga babban shafi
RSF

‘Yan Jarida 110 aka kashe a 2015

Kungiyar da ke kare hakkin ‘Yan jaridu a duniya ta Reporters Without Borders tace ‘yan Jaridu 110 aka kashe a cikin shekarar 2015 a fadin duniya tare da yin gargadi akan yadda ake kisan ‘Yan jaridun da gangan.

'Yan Jaridu na fuskantar kalubale a duniya
'Yan Jaridu na fuskantar kalubale a duniya RSF
Talla

Rahoton da kungiyar ta fitar a yau Talata, ta ce ‘Yan Jaridu 67 aka kashe lokacin da suke gudanar ayyukansu a bana, sannan an kashe wasu 43 ta hanyoyin da ba a gamsu da su ba.

A cikin rahoton, kungiyar ta bayyana rawar da kungiyoyin da ke da’awar jihadi ke takawa wajen aikata munana laifuka akan ‘yan Jaridu.

Sakatare Janar na kungiyar Christophe Deloire yace adadin ya dada fito da yadda ‘Yan Jaridu ba su samun kariya wajen gudanar da ayyukansu.

Kungiyar tace kashi biyu bisa uku na ‘Yan Jaridun da aka kashe bara sun mutu ne a inda suke gudanar da aiki wuraren tashin hankali, amma a shekarar 2015 sun mutu ne a kasashen da ake ganin suna zaman lafiya.

Kungiyar ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta gaggauta daukar matakan kariya ga ‘Yan Jaridu.

Kungiyar ta bayyana kasashen Iraqi da Syria a matsayin mafi hatsari ga ‘Yan Jarida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.