Masana kimiyar yanayi sun yi na’am da yarjejeniyar da aka cim ma
Masana kimiyar yanayi sun yi na’am da yarjejeniyar da aka cim ma ta rage dumamar yanayi a Paris, amma sun ce har yanzu akwai gibi, ga bayanin tsarin yadda kasashe zasu rage gurbataccen iska da ke haifar da matsalar.
Wallafawa ranar:
A ranar Asabar ne kasashe 195 suka amince da yarjejeniyar da ta kunshi rage dumamar yanayin zuwa kasa da biyu na ma’aunin yanayi.
Masanan na ganin akwai bukatar a rage fitar da dattin hayaki da masana’antu ke fitarwa da kusan kashi 70 zuwa 90 daga yanzu zuwa shekaru 50.
Yarjejeniyar da aka amince a Paris ta shiga cikin kundin tarihi a duniya inda ake ganin matsalar dumamar yanayi babbar matsala ce ga rayuwar bil’adama.
China mai yawan fitar da gurbsataccen iska ta yi na’am da yarjejeniyar .
Shugaban Amurka Barack Obama yace wannan dama ce ta ceto duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu