Isa ga babban shafi
Faransa

Kasashen duniya sun tsawaita taron sauyin yanayi

Wakilan kasashen duniya da ke tattaunawa kan matsalar sauyin yanayi a birnin Paris na Faransa sun ci gaba da neman hanyoyin da za su kai ga cimma yarjejeniyar rage dumamar yanayi da kashi 2 cikin 100 nan da shekara ta 2020.

Shugaban taron sauyin yanayi a Paris kuma Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius.
Shugaban taron sauyin yanayi a Paris kuma Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius. 照片来源:路透社REUTERS/Jacky Naegelen
Talla

Wannan na zuwa ne bayan shugaban taron kuma ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius ya sanar da tsawaita zaman taron zuwa gobe asabar.

Daya daga cikin batutuwan da ke haifar da tarnaki da kuma kasashen na duniya ke tattaunawa a kai shine kan yadda za a samar da kudaden yaki da dumamar yanayin.

Idan har kudiri na 6 da ke kunshe a kundin yarjejeniyar, wanda kuma ya tanadi samar da kudaden tafiyar da aikin, na tattare da shakku da ya sa bangarorin kasa yin kai daya a kansa, to ya zama wajibi su koma tattaunawar neman wata sabuwar yarjejeniya.

Rikita rikitar dai ta kasance ne a jimlar farko ta kundin yarjejeniyar na alkawuran da kasashe masu arzikin masana’antu su ka dauka na tallafa wa matalautan kasashe na ba su tallafin kudaden rage kaifin illar da dumamar yanayi ta haddasa mu su, a karkashin sabuwar yarjejeniyar da ake son a cimma.

Suma dai kasashe masu tasowa sun taso da batutuwan da ke neman kasashen ma su arzikin masana’antun sun cika alkawuran da suka dauka a taron dumamar yanayi na Copenhagen a 2009, na bai wa kasashe matalautan da dumamar yanayin tafi yi wa illa tallafin dalar Amurka biliyan 100, domin zama wata manuniyar da ke tabbatar da cewa za a iya cimma nasarar shirin na rage dumamar duniya da 2 cikin 100 nan da 2020.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.