Isa ga babban shafi
Austria

Australia ta tuhumi matasa akan ta'addanci

Hukumomin Australia sun tuhumi wasu mutane biyar cikinsu har da mai shekaru 15 bisa zargin su da shirya kaddamar da harin ta’addanci a wani ginin gwamnati.

Jami'an tsaron Australia da ke yaki da aikin ta'addanci
Jami'an tsaron Australia da ke yaki da aikin ta'addanci REUTERS/David Gray
Talla

A sanyin safiyar yau ne jamai’an tsaron kasar suka cafke matashin mai shekaru 15 da kuma wani dan shekara 20 bayan sun kai samame a gidajensu.

Tuni dai aka maka wasu matasa uku dabam gidan yari bayan an tuhume su bisa wannan yunkurin na kai hari kuma duk ba su haura shekaru 23 ba.

Wannan dai ya biyo bayan shaidun da hukumomin kasar suka tattara ne a shekarar da ta gabata, inda suka kama tare da tsare mutane 15 da ake zargi da aikin ta’addanci.

An dai gudanar da bincike ne sakamakon rahoton leken asiri da aka fitar a bara, inda aka bayyana cewa wasu masu ra’ayin rikau na shirin kaddamar da hare hare a Australia.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.