Isa ga babban shafi
Amurka

Dan bindigarda ya kashe mutane 3 a Coloradon Amruka na kyamar zubarda ciki ne.

Makashin nan, da ya hallaka mutane uku a cibiyar kula da tsarin iyali ta jihar Colorado a yammacin kasar Amruka, na adawa ne da tsarin zubar da ciki da cibiyar ke yi.

AFP
Talla

Masayar harbe harben da ta barke tsakaninsa da yan sanda a ranar juma’ar da ta gabata, ta haifar da bacin rai ga shugaban kasar ta Amruka Barak Obama, da ya kara bayyana damuwa da kuma adawarsa ga ‘yancin mallakar manyan makaman yaki a tsakankanin fal’ummar kasar inda ya bukaci majalisun dokokin kasar su duba lamarin domin yiwa tumkar hanci.

Robert Lawis Dear, farar fata ne mai shekaru 57 a duniya, wanda a ranar juma’arda ta gabat ya kutsa kai a babbar cibiyar kula da tsarin iyali ta kasar Amruka (planning familial Planned Parenthood), dake jahar Colorado Spring, inda daga bisani ya buda wuta da bindiga nan take kuma ya kashe Dansanda guda da fararen hula 2, tare da yiwa wasu mutane 9 kananan raunuka, al’amarin da ya haifarda masayar wuta ta tsawon awowi 5 tsakaninsa da jami’an tsaro kafin a kamashi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.