Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari zai halarci taron sauyin yanayi a Paris

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na daga cikin sugabannin kasashen duniya 80 da za su halarci taron sauyin yanayi da za a fara ranar litinin a birnin Paris na kasar Faransa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Faransa, Francois Hollande
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Faransa, Francois Hollande AFP PHOTO / DOMINIQUE FAGET
Talla

A hirarsa da RFI hausa, karamin ministan ma’aikatar muhallin kasar Ibrahim Usman Jibrin ya ce tuni ministar muhalli Amina Ibrahim ta isa Paris don shirya ziyarar shugaban.

Ministan ya yi karin bayani game da matsalolin muhalli a Najeriya, inda ya ce hamada ce babbar matsalar da tafi addabar wasu sassa a yankin Arewacin kasar, inda kuma yankin kudanci ke fuskantar barazanar ambaliyar ruwa saboda kusanci da teku wanda ke ci gaba yawaita saboda matsalar sauyin yanayi a duniya baki daya.

Ministan ya ce, narkewar kankara a Arewacin duniya na haifar da karuwar ruwan teku, lamarin da ke baraza ga al-ummar duniya baki daya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.