Isa ga babban shafi
Rasha-Turkiyya

Putin ya gargadi Turkiyya kan kakabo musu jirgi

Shugaban Russia Vladmir Putin ya gargadi Hukumomin kasar Turkiyya da su shiga taitayinsu, bayan da Turkiyya ta kakkabo wani jirgin Rasha da ke sintiri a kan iyakan kasar Syria.

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin REUTERS/Alexei Nikolskyi/SPUTNIK
Talla

Vladmir Putin Ya ce danganka tsakanin kasashen biyu na iya yin tsami.

Kallaman Putin da ke zuwa yayin ganawa da Sarki Abdalla na biyu na Jordan , ya ce wannan harbor mata jirgi da ke yakar ‘yan taadda na nuna cewa sojan Turkiyya na goyon bayan masu ra’ayin kungiyar Jihadi ta ISIS..

A halinda ake ciki dai kasar Rasha ta gargadi ‘yan kasar ta da su kiyaye da ziyara zuwa kasar Turkiyya.

Ministan waje Rasha Sergei Lavrov ya soke ziyarar da aka shirya za shi Turkiyya don tattaunawa da abokin aikinsa da ke chan a gobe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.