Isa ga babban shafi
Belarus-Rasha

Alexander Lukashenko ya sake lashe zaben shugabanci kasar Belarus

Shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko ya sake lase zaben shugaban kasar a karo na biyar, inda ya gargadi yan adawar kasar su kaucewa yin zanga zanga da zata sanya kasashen Turai kin cirewa kasar takunkumi.

Shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko
Shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko REUTERS/Maxim Shipenkov
Talla

Lukashenko ya samu kashi 83 na kuri’un da aka kada, kamar yadda shugabar hukumar zaben Lidiya Yermoshina ta sanar, yayin da wadda ta zo ta biyu Tatiana Korotkovich ta samu kusan kasi 5 na kuri’un.

Lukashenko mai shekaru 61 ya kwase shekaru 21 a karagar mulki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.