Isa ga babban shafi
Syria

Jiragen Rasha sun kashe fararan hula a Syria

An samu hasarar rayukan fararan hula a Kasar Syria sakamakon haren haren da jiragen yakin Rasha suka kaddamar a Hama da kuma yankin dake kan iyakar Idlib a safiyar yau laraba. 

A makon da ya gabata ne Rasha ta fara kaddamar da hare haren sama a Syria da nufin kawar da masu tayar da kayar baya.
A makon da ya gabata ne Rasha ta fara kaddamar da hare haren sama a Syria da nufin kawar da masu tayar da kayar baya. REUTERS/Ministry of Defence of the Russian Federation
Talla

Hukumar dake sa ido kan hakkin bil-adama a Syria wadda ke da cibiya a Birtaniya, ta bayyana cewa, rundunar Rasha ta kaddamar da hare haren ne domin ci gaba da far wa masu hamayya da gwamnatin Syria.

Masu fafutukar kare hakkin dan adam sun ce akalla mutane hudu sun rasa rayukansu sakamakon hare haren na yau, yayin da wasu da dama suka jikkata kuma akwai yiwuwar samun karuwar adadin wanda suka mutu a hare haren.

A makon da ya gabata ne Kasar Rasha da ta kasance aminiyar gwamnatin Bashar al-Assad ta fara kaddamar da hare haren jiragen sama a kasar ta Syria da nufin kawar da masu tayar da kayar baya.

A ranar talatar da ta gabata ne Jiragen su ka yi lugudan wuta a yankunan da ke karkashin ikon mayakan ISIS a Palmyra da kuma arewacin Aleppo.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.