Ana ci gaba da neman Alhazai a Saudiya
Daruruwan Alhazai ne ake ci gaba da nema a kasar Saudiya sama da mako guda bayan tirmitsitsin da aka samu wanda ya hallaka mutane da dama.
Wallafawa ranar:
Su dai hukumomin Saudiya sun bada sanarwar cewar mutane 769 ne suka mutu, yayin da wasu 934 suka samu raunuka a mummunan hadarin, ba tare da bada addin wadanda suka bata ba.
Sai dai wasu alkaluma na dabam sun nuna cewar wadanda suka mutu daga kasahse 24 sun kai 995, inda kasar Iran kawai ta ce ta rasa mutane 464, sai kuma kasar Masar da ta ce ta rasa Alhazai 124.
Najeriya ta tababtar da mutuwar alhazai 64, yayin da tace har yanzu bata ji duriyar wasu 244, yayin da kasar Mali ta rasa Alhazai 60, Indonesia 59, India 51 sai kuma Pakistan mai 46.
Jamhuriyar Nijar ta sanar da samun karin wadanda suka rasu daga 22 na adadin fako, sai Kamaru mai Alhazai 20, Chadi 11 da Ghana 8.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu