Faransa za ta gana da UAE kan rikicin Syria
Ministan tsaron Faransa Jean Yves Le Drian zai yi wata ganawa da Hadaddiyar Daular Larabawa kan yadda za’a fuskanci mayakan kungiyar ISIS a kasar Syria.
Wallafawa ranar:
Faransa ta ce nan gaba kadan za ta kaddamar da hare haren sama kan mayakan dake da’awar jihadi wadanda ayyukansu suka dada jefa kasar cikin halin kunci.
Har ila yau tashe tashen hankulan na Syria su suka kuma haifar da dubban ‘yan gudun hijirar da yanzu haka suka kwarara zuwa Turai.
A jiya lahadi ne Le Drian ya isa Hadaddiyar Daular Larabawa kuma ana sa ran zai tabo batun rikicin Kasar Yemen a ganawar da zai yi da mahukuntan Daular.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu