Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka na tunawa da mutuwar 'Yan Kasar bayan shekaru 14

Kasar Amurka ta yi juyayin hasarar rayukan da aka yi a haren haren ta’addanci da aka kaddamar a Kasar a ranar talata, 11 ga watan Satumban shekarar 2001. 

Shugaban Amurka Barack Obama da Uwargidansa Michelle Obama lokacin da suka yi shiru na tsawon minti guda domin tunawa da 'Yan Kasar da hare haren suka ritsa da su
Shugaban Amurka Barack Obama da Uwargidansa Michelle Obama lokacin da suka yi shiru na tsawon minti guda domin tunawa da 'Yan Kasar da hare haren suka ritsa da su REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Shekaru 14 kenan da aka yi amfani da jiragen sama wajan kai hare haren a cibiyar kasuwani ta duniya dake birnin New York na Amurka yayin da akalla mutane dubu 3 suka rasa raykansu

Tuni dai gwamantin Amurka ta zargi Kungiyar Al-Qaeda da kitsa hare haren wadanda suka yi sanadiyar rubtawar gine ginen na cibiyar kasuwancin mai hawa sama da 100.

Shugaba Barack Obama da Uwargidansa Michelle Obama sun yi shiru na tsawon minti guda a fadar White Housa domnin tunawa da wadanda suka rasa rayukansu a hare haren.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.