Isa ga babban shafi
Guatemala

An fara gudanar da babban zabe a kasar Guatemala

Dazun nan aka bude rumfunan zaben kasar Guatemala, inda za a gudanar da babban zaben kasar, yayin da jama’a bayyana shakku kan sahihancin shugabannin da zasu zaba a nan gaba.

Masu zanga zanga a kasar Guatemala
Masu zanga zanga a kasar Guatemala AFP PHOTO / ORLANDO ESTRADA
Talla

Wannan na zuwa ne ‘yan kwanaki kadan, bayan yanke wa tsohon shugaban kasar Otto Perez, hukuncin dauri a gidan yari, bayan da aka same shi da laifin cin hanci.
Da misalin karfe daya na rana agogon GMT aka fara zabe, inda ‘yan kasar miliyon 7 da rabi, da suka cancanci kada kuri’a, zasu fidda sabon shugaba da mataiamakinsa, ‘yan majalisar dokoki, da kuma magadan gari 338.
Sai dai har yanzu akwai yuwuwar samun zanga zangar nuna kyamar ayyukan cin hanci da rashawa, duk da zabukan dake gudana.
Magoya bayan wasu jam’iyyun siyasar kasar sun gwabza rikici jiya Asabar, lamarin da yayi sanadiyyar rasa ran mutum guda, aka kuma kama wasu 26 a garin Santa Barbara, dake kudancin kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.