Isa ga babban shafi
Amurka

Wasa ya zama fada a makarantar horas da sojojin kasar Amurka

Wasu matasan dake samun horo a makarantar horas da jami’an sojan Amurka sun sami raunuka, bayan da wani wasa fada da matashin kai wato Pillow, ya rikide zuwa wani abu daban.

wasu sojoji suna cikin farin ciki
wasu sojoji suna cikin farin ciki REUTERS/Tami Chappell
Talla

Rahotanni na cewa wasu daga cikin matasan, sun zuba hular kwano a cikin matasan kan, a ranar wasan, da itace ta karshe a shekarar karatun bana, inda suka yi ta rafka wa abokan wasan nasu.
Ana dai basu hular kwanon ne don su sanyata a matsayin kariya, ranar wasan pillow, amma wannan karon wasu suka yita amfani da ita a matsayin madaki, kan ‘yan uwansu.
Yanzu an ce lamarin yayi sanadiyyar raunata matasa 30,
Da suka hada da wani da ya smi karaya, da kuma wanda aka targada.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.