Isa ga babban shafi
Taliban

Taliban ta fadi dalilin da ya sa ta boye labarin mutuwar Mullah Omar

Kungiyar Taliban ta tabbatar da boye labarin mutuwar Mullah Omar wanda ya mutu tsawon shekaru biyu da suka gabata kafin jami’an leken asirin Afghanistan su sanar da mutuwarsa a bana.

Sabon Shugaban Taliban Mullah Akhtar Mohammad Mansour
Sabon Shugaban Taliban Mullah Akhtar Mohammad Mansour REUTERS/Taliban Handout
Talla

A ranar 30 ga watan Yuli ne Taliban ta tabbatar da cewa Mullah Omar ya mutu, amma ba tare da cikakken bayani akai ba.

Amma a sanarwar da kungiyar ta fitar a yau Litinin, Taliban ta tabbatar da cewa Mullah Omar ya rasu ne a ranar 23 ga watan Afrilu na 2013.

Sanarwar tace an boye labarin mutuwarsa ne tsakanin manyan shugabannin Taliban.

A cikin sanarwar, Taliban ta ce ta boye sanar da mutuwar shugaban ne a 2013 saboda shirin dakarun kasashen waje na ficewa daga Afghanistan a karshen 2014.

Amma wasu na ganin rikicin shugabanci tsakanin mambobin Taliban ne ya sa aka boye labarin mutuwar Mullah Omar.

Yanzu haka kuma wasu shugabannin Taliban da suka hada ‘yan uwan Mullah Omar sun ki yin mubaya’a ga sabon shugaban kungiyar Akthar Mansour.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.