Isa ga babban shafi
AMURKA-KATARINA

A yau ake tunawa da shekaru 10 da ratsawar Guguwar Katarina a Amurka

Shekaru 10 bayan ratsawar guguwar Katrina a kasar Amruka a yau assabar 29 ga watan Ogusta ne ake gudanar da tunawa da mahaukaciyar guguwar da kada a Nouvelle Orléans na kasar ta Amruka

barnar da guguwar Katrina ta haddasa a   Nouvelle Orléans a 29/8/2005.
barnar da guguwar Katrina ta haddasa a Nouvelle Orléans a 29/8/2005. U.S. Coast Guard/Kyle Niemi
Talla

Idan dai ba a manta ba a daidai rana irin ta yau 29 ga watan Ogustan shekara ta 2005 ne, guguwar ta Katrina ta ratsa jahar Louisiana ta kasar Amruka inda ta yi sanadiyar mutuwar kimanin mutane dubu 1800 tare da lalata sama da kashi 80 cikin 100 na yankin bakin tekun da ta ratsa, a yayinda Nouvelle Orléans ya zama garin da yafi lalacewa da hasarar rayuka a cikin guguwar

kasar Amruka dai na daya daga cikin kasashen duniya dake fuskantar irin wannan bala'i da  gurbatar yanayi ke haddasawa inda kusan a ko wace shekara take fuskantar ko dai bala'i daga Ambaliyar Ruwan sama, ko Wutar Daji, ko kuma na tsananin Sanyin Hunturu

A dai gefen kuma guguwar Erika dake tafe da iska mai karfi, da ruwan sama kamar da bakin kwarya, ta ratsa kasar Haiti a cikin daren jiya  kawo safiyar yau assabar,  bayan da ta tabka barna a tsibirin Dominican tare da kashe mutane sama da 20

Sakamakon farko da gwamnatin Haiti ta bayar ta nuna cewa, mutane 3 ne suka jikkata a wani gida da ya ruguje a  birnin  Port au Prince babban birnin kasar
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.