Isa ga babban shafi
MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar da sabon shirin yaki da talauci a duniya

Majalisar dinkin duniya ta amince da wani sabon tsarin fara tara adadin kudin da ya kai dala triliyan 3.5 zuwa 5 domin bunkasa rayuwar al’ummar da talauci ya yiwa katutu a duniya.

Sakatare janar na MDD Ban Ki-moon
Sakatare janar na MDD Ban Ki-moon REUTERS/Eduardo Munoz
Talla

Matakin da ke zuwa yayin wani taron shirin bunkasa rayuwar al’umma da majalisar ta gudanar tare da kasashen 193 da ta ke aiki tare da su a karshen wannan mako, ana saran samun amincewar saura shugabannin kasahsen duniya a taron da za su gudanar tsakanin 25 da 27 na watan Satumba mai zuwa.

Sabbin kudirorin Majalisar 17 sun hada da kawo karshen talauci a duniya, samar da ingantaccen lafiya, bunkasa ilimi da kuma yaki da kwararowar Hamada wadanda suka zarce muradun karnin da ke karewa a karshen wannan shekara.

Sakatare Janar na Majalisar Ban Ki Moon ya bayyana sabbin kudirorin a matsayin masu muhimmanci ga rayuwar jama’a da kuma duniyar kan ta, sai dai ya ce aiwatar da su ba karamin aiki bane.

Jakadan kasar Kenya Macharia Kamau wanda ya jagoranci tattaunawar amincewar daftarin tare da Jakadan kasar Ireland David Donoghue ya bayyana cewa tara kudadden aiwatar da kudirorin babban kalubale ne ga kasashen duniya.

Kamau ya ce bukatar su ita ce tababtar da cewa an shiryar turbar kawar da matsalolin tattalin arziki, jin dadin rayuwa da kuma inganta muhalli.

Sai dai Bill da Milinda Gates da ke da gidauniyar taimakawa al’umma sun bayyana sabon shirin a matsayin wanda ya kaucewa na samar da ilimi da lafiyar al’umma da aka saba da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.