Isa ga babban shafi
Faransa-Malaysia

Ana dakon sakamakon bincike da ake gudanarwa kan bacewar jirgin Malaysia

Ana sa ran masu bincke da ke kasar Faransa za su sanar da sakamakon binciken da suka gudanar, ko banagaren da aka samu a tekun India na jirgin saman fasinjan nan ne na Malaysia da ya fadi tun bara dauke da fasinjoji 239 .

Talla

Jirgin saman mai lamba MH17 mallakin kasar Malaysia ne, kuma bacewa yayi ranar 8 ga watan uku na shekarar da ta gabata, kuma tun lokacin ake ta cigiyan jirgin amma babu ko alamun inda ya shiga.

A makon jiya ne dai aka ga wani abu mai kama da bangaren jirgin yana yawo a tekun  La Re-union na India, kuma nan da nan aka kwasa aka mika zuwa Faransa domin tattancewa ko na wancan jirgin sama ne da ya bata tun bara.

Gwanayen bincike da ke yankin Toulous na Faransan , kuma majiyoyi a Faransa na cewa babu shakka duniya za ta sani ko wancan abu da aka gani daga jikin wancan jirgi ne, kuma da Karin haske game da abinda ya faru.

Bayanai na nuni da cewa za’a baje dukkan bayanai a gobe laraba gaban kowa, da suka hada da wakilan kamfanin Boeing da suka kera jirgin, da dangi da ‘yan uwan fasinjojin wadan da yawanci daga kasar China suke.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.