Isa ga babban shafi
Amurka-Masar

Yarjejeniyar Iran ta shafi zaman lafiya a Gabas ta tsakiya- Kerry

Sakataren harakokin wajen Amurka John kerry ya jaddada wa kasashen gabas ta tsakiya aminnnan Amurka cewa su kwantar da hankalinsu yarjejeniyar nukiliya da suka amince da Iran ba za ta haifar da wata barazana ba ga kasashen.

John Kerry na Amurka tare da Ministan harakokin wajen Masar Sameh Shukri
John Kerry na Amurka tare da Ministan harakokin wajen Masar Sameh Shukri Reuters
Talla

Kerry ya yi wannan furuci ne a yayin da ya isa Masar, a ziyarar da ya fara a yankin gabas ta tsakiya a jiya Lahadi.

Masar da Saudiya dai na dari-dari da yarjejeniyar da manyan kasashen duniya suka amince da Iran, amma Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry ya jaddada wa kasashen su kwantar da hankalinsu domin yarjejeniyar ba za ta haifar da wata barazana ba gare su.

Kasashen dai na ganin amincewa da yarjejeniyar Iran dama ce na karawa kasar karfi a gabas ta tsakiya.

Kerry ya shaidawa manema labarai cewa yarjejeniyar nukiliyan Iran ba zata zama barazana kasashen Larabawa ba.

A jiya Lahadi ne Kerry ya isa Masar inda ya gana da shugabba Abdel Fattah al-Sisi, kafin ya nufi Qatar.

Dandagta dai tsakanin Amurka da Masar ta dada lalacewa tun lokacin da sojoji karkashin jagorancin shugaba na yanzu suka hambarar da gwamnatin ‘yan uwa musulmi ta Mohammed Morsi a 2013.

Kerry kuma ya bukaci mahukuntan Masar su mutunta hakkkin bil’adama a yayin yaki da masu tayar da kayar baya a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.