John Kerry zai ganawa da shugaban Masar a yau
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya samu isowa kasar Masar, Ziyarar da za ta bashi damar ganawa da Abdel Fattah al-Sisi don duba batutuwan tsaro dama yadda za a tunkarin mayakan IS da ke da’awar Jihadi a duniya.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A dai wajen Shugabannin za su tattauna kan batutuwan da suka shafi matsalar tattalin arziki,diflomasiya dama batutuwan kare hakin bil adam a kasar Masar.
Amurka na daya daga cikin mayan kasashe a Duniya dake bayar da gudunmuwa zuwa masar kan batutuwan da suka shafi tsaro,tareda bayar da horo zuwa dakarun Masar.
Akwai yiyuwar dai Sojojin Masar zasu kulla kawance da Amurka domin yakar Mayakan IS a Iraqi.
John Kerry bayan kasar Masar zai kai ziyara wasu kasashen Asiya dama yankin gabas ta tsakiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu