Isa ga babban shafi
Rasha

Rasha ta hau kujerar na-ki kan binciken jirgin Malaysia a Ukraine

Kasar Rasha ta hau kujerar na-ki, dangane da wani kuduri da Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a amince da shi domin kafa kotun kasa da kasa da za ta yi aikin bincike tare da hukunta wadanda ake zargi da harbo jirgin Malaysia a wani yanki gabashin Ukraine, inda mutane 298 suka mutu.

Sama da Shekara guda da aka harbo jirgin Malaysia a Ukraine
Sama da Shekara guda da aka harbo jirgin Malaysia a Ukraine Reuters
Talla

Kasashen duniya na zargin cewa ‘yan aware a yankin gabashin Ukraine ne suka harbo jirgin lokacin da ya ke ratsa sararin samaniyar kasar, amma Rasha ta ce za ta gabatar da wani daftarin na daban a game da wannan batu zuwa ga Majalisar Dinkin Duniya.

Mambobin kwamitin tsaro 15 ne suka amince da daftarin bukatar a gudanar da bincike akn harbo jirgin mai lamba MH17, kudirin da Australia da Belguim da Malaysia da Holland da Ukraine suka gabatar.

Kuma kudirin ya samu amincewar Birtaniya da da Faransa da Amurka da suke zargin ‘Yan tawayen Ukraine ne suka harbo jirgin da babban makamin da Rasha ta ba su.

Rasha dai ta dade tana musanta zargin tana da hannu a rikicin Ukraine.

A ranar 17 ga watan Yulin 2014 ne aka harbo Jirgin a yankin Ukraine, kuma yawancin wadanda suka mutu a jirgin ‘Yan kasar Australia ne da Holland.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.