Isa ga babban shafi
kimiya

Gargadi game da kera mutum mutumi a matsayin makami

Kwararri kan a bangaren kimiya sun yi gargadi game da shirin cigaba da kera mutum mutumi da ake yi a matsayin wani makami na yaki, mutum mutumin dai na iya aiwatar da duk wani sako ba tare da sa hannun dan adam ba.

Wani mutum mutumi a kasar Faransa
Wani mutum mutumi a kasar Faransa AFP PHOTO / BERTRAND GUAY
Talla

A wata sanarwa da suka fitar a wannan talata, jagorori a fannin ilimim kimiyar sun yi gargadi domin kaucewa amfani wajen sarrafa wannan makami na mutum mutumi da ka iya kai hari ba tare da dan adam ba.

A budadiyyar wasikar da masanan da yawansu ya kai dubu daya suka fitar sun bayyana mutum mutumin a maytsayim makami mafi illa ba ya ga harsashi ko makaman nukiliya.

Abin yi a cewar su shi ne a kaucewa kera irin wannan makami domin gudun duk wani tashin hankalin da za a a iya shiga gasar yin amfani da shi lokacin yaki akan juna.

Wannan makami na mutum mutumi dai ya shahara ne bayan an yi anfani da shi a wani fim mai suna ‘Terminator’ inda shararren dan fim Arnorld Schwarzenegger ya fito a matsayin mutum mutumin yana kai munanan hare hare kamar yadda aka umarce shi da ya yi.

Jagororin dai sun yi gargadi da cewa anfani da makamakin na tattare da hadurra ciki kuwa har da yiyuwar fadawarsa a hannun yan ta’ada.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.